23 ga watan Maris za’a kammala zabukan jahohi 6 – INEC

Hukumar zaben Najeriya INEC, ta ce a ranar Asabar 23 ga watan  Maris, za ta sake gudanar da zabuka a wasu mazabu da rumfunan zabe da ke jahohin Adamawa, Bauchi, Filato, Kano, Sokoto da kuma  Benue.

Hukumar zabe mai zaman  kana wato  INEC ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter, dauke da sa hannun daya daga cikin kwamishinoninta, Festus Okoye.

Sanarwar ta ce hukumar ta dauki matakin ne, bayan wani zama da ta yi  ranar Talata  12 ga watan Maris inda ta yi nazari kan yadda aka gudanar da zabuka a jahohi 29 da kuma mazabun ‘yan majalisar dokokin jaha 991, wadanda aka yi a ranar 9 ga watan Maris.

Hukumar ta ce, an ayyana zabukan a matsayin wadanda ba a kammala ba ne, saboda dalilai masu yawa, mafi aksari, saboda yadda aka daina amfani da na’ura mai tantance masu kada kuri’a ko kuma inda aka gaza kai na’urorin, ko kuma aka jefa kuri’u fiye da kima ko kuma aka samu hatsaniya a wasu rumfunan zaben

You might also like More from author

Comments are closed.