Abin da yasa Atiku guje wa taron zaman lafiya

Tsohon shugaban Najeriya Janar mai ritaya Abdussalam Abubakar wanda shi ne shugaban kwamitin kulla wannan yarjejeniyar ya bayyana cewar  kafin a gaudanar da taron sai da suka zauna tare da dukkannin jam’iyyun siyasa kasar ta Najeriya, sannan aka tsayar da ranar kulla yarjejeniyar.

Inda yace bai san dalilin da ya hana dan takarar ta shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP  wato Atiku Abubakar zuwa taron ba,inda ya kara da cewar rashin zuwan Atiku bazai hana komai ba.

Sai dai a bangaren na dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewar bai sanda taron  tabbatar da zaman lafiya a zaben 2019 ba domin ba’a gayyace shi ba.

Kakakinsa Paul Ibe ne ya fitar da sanarwar hakan a shafinsa na Twitter.”Babu wani goron gayyata da Atiku ya samu domin halartar taron kulla yarjejeniyar ta zaman lafiya,” in ji shi.

Yarjejeniyar da tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya ke jagoranta ta bukaci ‘yan takara da jam’iyyunsu su tabbatar da zaman lafiya a lokacin zabe da kuma bayan zaben.

Yarjejeniyar kuma ta bukaci a kaucewa duk wasu kalamai na batanci ga addinin wani ko kabila.

Sannan ta shafi kauracewa  duk wani abu da zai kai ga haifar da tashin hankulan al’umma  a lokacin zabe.

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: