An Bayyana Dalilin Da Ya Sa Rigingimun Ta’addanci Suke Yawaita A Kasashen Yammacin Afrika

Yawaitan tashe-tashen hankula da sunan ta’addanci a yankunan Sahel na yammacin Afrika, duk suna faruwa ne a sakamakon gazawar da hukumomin yankin suka yi na samar da ababen more rayuwar da suka wajaba da kuma tsaro.

Amma ba wai fahimta ce mai alaka da Addini ba. Wannan shi ne samakon binciken da wata kungiya, ‘Peace building charity International Alert has found,’ ta yi.

A bisa tattaunawar da kungiyar ta yi sosai da al’ummun Fulani a kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar, ya bayar da hasken dalilin da ke sanya wa matasansu ke shiga cikin kungiyoyin da suka dauki makamai. Marco Simonetti, shugaban kungiyar a yammacin Afrika cewa ya yi; “Yanda shugabanni a yankunan suke yin abin da suka ga dama da dukiyar al’umma ba tare da an iya yi masu komai ba, shi ke sanya wa masu tsattsauran ra’ayin ke amfani da hakan wajen jan ra’ayin matasa talakawan da ke cutuwa da hakan domin su shiga cikin su, da sunan kawo shari’a.

“A gaskiya, kiran kaddamar da Jihadi ba shi ne ainihi ba kan, tsare wa mutane masoyansu ba bisa ka’ida ba, ko kokarin kwace wa mutane wuraren yin kiwon su, ko neman shugabanci a kauyaku. Hakanan binciken ya gano, rashin aminta da gaskiyan jami’an tsaro da al’ummu ke yi, yakan sabbaba lalacewar harkar tsaro a yankunan. Sa’ilin kuma da talauci da rashin aikin yi ke kara yawaita, wanda a cewar rahoton duk hakan yana cikin abin da ke kai matasan gwammace shiga cikin kungiyoyin da suka dauki makaman. Wani da masu binciken suka tattauna da shi a kasar Nijar cewa ya yi; “Rashin aiki ga matasa shi ne babban dalilin da ke addabar mu…Hakan ne kuma ke sanya wa matasan tausaya wa kungiyoyin masu rike da makamai.”

“Kariya ga azzalumai da kuma tafiyar da tsarin da ke cike da zalunci ya fi ban takaici fiye da ayyukan na masu Jihadi,” in ji wani da aka tattauna da shi daga Nijar. Rahoton ya yi kira ga dukkanin kasashen da suke da bakin magana a kasashen na yankin Sahel, da su taimaka wa gwamnatocin kasashen wajen kokarin tabbatar da gaskiya a cikin gwamnatocin na su da kuma yin adalci ga ‘yan kasashen na su, da samar da daidaito a tsakaninsu, wanda duk rashin hakan ne ke sanya matasa tsunduma cikin kungiyoyin masu tsautsauran ra’ayi. Rahoton kuma ya nemi da a kara sanya ido kan hukumomin tsaro sosai a kuma samar da ayyukan yi ga matasa.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: