An fara rusa kasuwar Barci ta jahar Kaduna

Gwamnatin jahar Kaduna ta fara aikin rushe Kasuwar Barci bayan wa’adin kwana uku da ta bai wa mazauna kasuwar ya cika.

Tun a wayewar garin Asabar din da ta gabata ne mazauna kasuwar suka tarar da takardar wa’adi like gaban shagunansu inda gwamnatin jihar ta umarce su da su tattara su bar kasuwar.

Daraktan Hukumar Kula da Raya Birane ta Jihar Kaduna Ismail Dikko ya shaida wa BBC cewa gwamnatin jihar ta Kaduna na da burin sauya fasalin kasuwar ta yadda jama’a daga kasashen ketare za su rinka zuwa kasuwar domin gudanar da kasuwancinsu. .

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: