An hango gwaggwan birrai dauke da jarirai a kasar Najeriya

A karon farko cikin shekaru da dama an hango rukunin wasu gwaggwan birrai, wasu ma goye da jariransu, a kan wasu tsaunuka da ke kudancin Najeriya.

BBC ta rawaito cewa, masu kare gandun daji sun bayyana fatansu cewa gwagwan birran da aka dauko hotunansu a jihar Cross River za su ci gaba da hayayyafa duk da fargabar da ake yi cewa sun kusa karewa.

Kungiyar da ke kare gandun dazuka ta Wild Conservation Society in Nigeria, ta ce an dauki hotunan gwaggwa birran ne da wata na’urar daukar hoto da aka ajiye a matsayin tarko a farkon shekarar nan.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: