An kama mutane biyar da ake zargi da sayen katin zabe a Kano

Rudunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da kama wasu mutane biyar da take zargi da sayen katin zabe a unguwar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa a Jahar kano.

Kakakin rundunar a jihar DSP Abdullahi Haruna Kyawa, shi ne ya tabbatar wa da BBC hakan, inda ya ce an kama mutanen ne bayan da suka samu labari.
Mutanen dai sun hadar da mata da mata, kuma ba a karamar hukumar Nassarawar kadai aka samu irin wadannan mutanen ba, har da karamar hukumar Dala inji jami’in.
Ya ce, da kyar suka kwaci mutanen daga hannun mutanen unguwannin da suka je sayen katin zaben.

DSP Abdullahi Haruna Kyawa, ya ce, dama tuni sun fuskanci cewa akwai wasu laifuka da mutane kan aikata a lokuta kamar kafin zabe da laifukan lokacin zabe da kuma na kafin a karasa zabe wato irin yanayin da Kanon ke ciki ke nan.
Jami’in dan sandan ya ce yakamata mutane su sani cewa ‘ Hukumar ‘yan sanda na sanar da su cewa saye da sayar da katin zabe babban laifi ne’.
Ya ce laifin ba wai na masu sayen katin zaben ba ne kadai, har ma su kansu masu sayarwan suma ya shafe su.
DSP Abdullahi Haruna Kyawa, ya ce ‘ Zamu bi lungu da sako mu kamo duk wanda ya aikata irin wannan dabi’a, da wanda ya saya da ma wanda ya sayar dukkansu masu laifi ne, kuma za a yi bincike a kansu sannan a gurfanar da su a gaban shari’a’.
Jihar Kano dai ta shiga jerin gwanon jihohin da INEC ta bayyana cewa ba a kammala zaben ta ba, jihohin da suka hada da Adamawa da Benue da Sokoto da Bauchi da kuma Plateau.
Hukumar ta INEC ta sanar da cewa za a sake gudanar da zabukan a ranar 23 ga watan Maris, 2019 a jihohin da ta sanar da cewa ba a kammala zabensu ba.

You might also like More from author

Comments are closed.