An kashe mai yin garkuwa da mutane a Kawo

An  kashe wani mutum da a ke zargi da yin garkuwa da mutane a unguwar kawo da ke jahar Kaduna, inda mazauna yakin suka ce mutumin yazo unguwar ne da nufin yin garkuwa da wani mazaunin garin.

Rahotonin na nuna  cewa, a safiyar Litinin 20 ga watan Mayu 2019 da misalin karfe 8 ne mazauna unguwar suka samu rahoton cewa, wasu masu garkuwa da mutane su uku sun shigo unguwar, inda suke da shirin yin garkuwa da wasu mutanen yankin.

Hakan yasa mazauna yakin suka  rufe duk hanyoyin shiga unguwar, sun fatattaki wadanda ake zargin,

Mutum biyu ne suka rasu sakamakon afuwar lamarin.

You might also like More from author

Comments are closed.