An tsige kakakin majalisar Edo

Yan majalisar jihar Edo dake a kudu-maso-kudancin kasar nan a jiya sun tsige kakakin majalisar mai suna Mista Justin Okonoboh.

A jiya Litinin ne aka tsige kakakin majalisar bayan wani yamutsi da dauki ba dadi da aka shafe tsawon lokaci anayi a zauren majalisar.  yan majalisar sun bayar da laifukan rufe majalisar da kakalin yayi na tsawon lokaci domin ya je bukukuwan kammala karatun dansa da kuma bada kwangiloli ba bisa ka’ida ba a matsayin dalilan tsige shi. Tuni dai har yan majalisar sun zabi wanda zai maye gurbinsa mai suna Kabiru Adjoto wanda kuma ya fito ne daga mazabar Akoko-Edo I.

You might also like More from author

Comments are closed.