APC na siyan katin zabe ka N10, N20 da N50 – Atiku

Dan takarar shugaban  kasar Najeriya karkashin inuwa jam’iyyar PDP  Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi jam’iyyar APC mai mulkin kasar da sayen katunan zabe.

Atiku ya yi zargin ne a birnin Ilorin a jahar Kwara inda ya kaddamar da yakin neman zabensa na shiyyar arewa ta tsakiyar ranar Laraba 5 ga watan Disamba, inda yace ana sayen katunan zabe, a kan N10, N20 ko kuma N50.

Shin mutane suna so su sayar da  makomarku ne? Toh idan har kuka sayar da katin zabenku za’a yi amfani da su wajen yi muku abun da ba daidai ba.

Sai dai APC ba ta ce komai a kan zargin ba.

 

 

You might also like More from author

Comments are closed.