APC Ta Yi Nasara A Zaman Kuton Farko Kan Zaben Bauchi

Lauyan kotu korafe-korafe  ka zabe  na jam’iyyar APC yayi kalubalai kan cewa akwai aringizon kuri’u a kananan hukumomin Tafawa-Balewa, Bogoro da Bauchi, kuma sun je sun kirga kuri’un tare da tabbatar da haka bisa binciken na’urorin zabe, wato Card Reader,kuma sun yi hakan ne a gaban lauyoyin jam’iyyar PDP.

Inda   alkali yayi tambayi ga lauyan jam’iyyar PDP cewa ya yarda da kalubalan da suke yi a kan zaben? Sai dai  bai musanta hakan ba.

Amma ya nemi alfarmar kotu da ta dage shari’ar zuwa ranar 2 ga watan 7 2019.Da haka  Alkali ya dage shari’ar zuwa 27 ga watan Mayu don ci gaba da shari’ar.

Jam’iyyar APC reshen jahar Bauchi na cigaba da sauraren kotu,inda take kalubalantar nasarar da jam’iyyar PDP ta yi a zaben gwanma.

You might also like More from author

Comments are closed.