Atiku ne yace zabe kuma zamu karba a kotu – PDP

Sakataren PDP, Sanata Umar Tsauri, ya ce jam’iyyarsu sam ba ta amince da kuri’un da a ka sanar shugaba Buhari ya samu ba, ya na mai zargin a wasu wajajen ma rubuta kuri’a a ka yi. Shi ma kakakin kamfen na jam’iyyar, Buba Galadima, ya ce ya na da kwarin gwiwar cewa muddun za a yi shari’ar adalci, to tabbas  PDP za ta koma fadar Aso Rock

An bude wani sabon babi a takaddamar sakamakon zaben Shugaban Kasa a Najeriya, bayan da jam’iyyar PDP ta shigar da kara a kotun daukaka kara don kalubalantar ayyana Shugaba Buhari na jam’iyyar APC da aka yi a matsayin wanda ya ci zaben.

 Kamar yadda ta ce za ta yi, babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta garzaya kotu, inda ta gabatar da takardun kararta kan ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya ci zaben Shugaban kasa, a maimakon gwaninta Alhaji Atiku Abubakar, wanda ta ce shi ya ci zaben.

Da ya ke karin bayani kan kalubalantar ayyana Buhari a matsayin wanda ya ci zaben Shugaban kasa da Hukumar Zaben Najeriya wato (INEC) ta yi, daya daga cikin lauyoyin jam’iyyar PDP Mike Ezekhome yace, “Mu na da kwararan hujjoji da mu ka dogara da su don karbar nasarar mu a mayarwa Atiku Abubakar shaidar lashe zabe.”

PDP ta kai karar ne a kotun daukaka kara, inda ake kyautata zaton daga nan shari’ar za ta yi ta tafiya har ta kare a kotun koli, kamar yadda tsarin yake.

Amma a daya gefen kuma, Ministan Shari’a kuma Attoni-Janar din Najeriya, Abubakar Malami, ya ce a shirye gwamnatin APC ta ke ta kare nasarar da ta yi na zaben Shugaban kasa a kotu.

Akashe ya kara da cewa zuwa kotu ba bakon abu ba ne ga Shugaba Buhari.

You might also like More from author

Comments are closed.