Atiku ya rattaba hannu a yarjejeniyar zaman lafiya

Dan takarar shugaban kasar Najeriya  karkashin babbar jamiyyar adawa ta  PDP,Atiku Abubakar ya rattaba hannu a kan takardar yarjejeniyar zaman lafiya, na zabukan masu gabatowa na 2019.

Shugaban jam’iyyar ta PDP Uche Secondus ne ya bayyana haka a shafinsa na Tiwita.

Mista Secondus ya bayyana cewa ya jagoranci Atiku Abubakar zuwa cibiyar Bishop Kukah da ke Abuja inda ya rattaba  hannu a kan yarjejeniyar.

Saidai Atiku Abubkar ya guje wa  taron  duk da cewa tsohon shugaban Najeriya Abdussalam Abubakar shi ne ya  jagoranci taron gudanarwar, kuma  kwamitinsa ta gayyaci dukkan jam’iyyun siyasar kasar zuwa wajen taron.

 

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: