Bana Siyasa amma idan na jefa maka kuri’a ba ka yi abunda ya dace ba zan fito nayi magana- Rahama Sadau

Menene ra’ayin ku game da hakkan? Duba da cewa abukan sana’arta da dama su tsunduma cikin Siyasa.

Shaharariyar jaruma Rahama Sadau
ta bayyana cewa,  ita ba ta siyasa, kila  a nan gaba tana iya  fara siyasa, amma a yanzu a’a.

“Ni na san wanda na zaba ba sai  na zo na nuna cewa ni na zabi wane ba. Yar Najeriya ce ni  kamar kowa duk abinda  na ga  ya yi mini  zan iya magana a kai. ” in ji ta.

Ta ci gaba da cewa “idan na jefa maka kuri’a, amma sai ka ki yin abin da ya kamata to zan fito na yi magana.”

Sadau ta bayyana hakkan ne a lokacin da take hira ta kai tsaya da BBC hausa

Batun yadda ake yawan ce-ce-ku-ce a kanta.
Ga abunda tace👇

Rahama ta ce hakan yana faruwa ne saboda yadda “duk abin da na yi duk kankantarsa mutane sai sun yi magana a kai.”

Rahama ta ce hakan ba ya sa ta damuwa “saboda mafiyawanci ban cika gani ba.”

“Idan na ga mutum daya ya fara magana mara dadi, fita nake yi gaba daya. Ba na ganin sauran, sai komai ya yi sauki. Wani lokacin kuma ina gani ban zan iya sa abu ya dame ni ba, abin da bai kai ya kawo ba,”a cewarta.

Batu na  Fyade kuma ga abunda shima tace👇

Ta ce ba ta jin dadin yadda matsalar fyade take ci gaba tabarbarewa, ta ce abin yana daure maka kai.
“Nakan tambayi mutane wannan abin da ke faruwa da gaske ne… wasu za ka ga ‘ya’yansu suke wa. Wai duk na mene ne,” in ji ta.

Ta ci gaba da cewa “wannan abin bacin rai ne ba kadan ba.”
Inda a karshe ta bukaci hukumomi da su dauki manyan matakai don dakile matsalar,  kuma ta ce ya kamata kowa ya tashi tsaye kan batun.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: