Buhari ya ba da umarnin gurfanar da Babachir da Oke a gaban kotu

oaktvhausaShugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin gurfanar da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal da tsohon darakta janar na hukumar bayanan sirri ta kasa Ayo Oke.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan jiya a Lagos lokacin da ya halarci wani taro da matasa mabiya addinin kirista suka shirya.
An dai kori Babachir daga aiki bayan da aka zarge shi da ba da kwangila ga wani kamfani da ya ke da alaka da shi, shi kuma Oke an kore shi ne sakamakon zargin da EFCC ta yi masa na yin sama da fadi da kudi dalar Amurka miliyan $43.4.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: