Buhari Ya Kaddamar Da Jirgin Kasan A Birnin Abuja

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da tsarin jirgin kasa mai sauki na fasinja da zai dinga zirga-zirga a cikin birnin tarayyar kasar, Abuja.

Shugaban ya kaddamar da jirgin ne a  yau  Alhamis 12 ga watan Yuli wanda shi ne kashi na farko na wannan aiki.

Hotunan da gwamnatin ta wallafa sun nuna shugaban a babbar tashar jirgin da ke Cibiyar Kasuwanci ta Duniya da ke tsakiyar birnin Abuja.

An shafe shekara 11 ana wannan “gagarumin” aikin tun zamanin mulkin gwamnatocin PDP, amma sai a zamanin Shugaba Buhari aka karasa shi.

A wancan lokacin aikin ya kai kashi 63 cikin 100, inda wannan gwamnatin ta kammala sauran kashi 37 din.

Tsarin jirgin ya kunshi tasoshi 12 a birnin tarayyar.

Hukumomi a Najeriya sun ce jirgin mai tsawon fiye da kilomita 45, shi ne irin sa na farko a yammacin Afirka.

Jirgin kasan zai dinga zirga-zirga ne a cikin birnin tarayyar har zuwa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe.

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: