Coronavirus: Ba’a suma hadin kan majilasa  kan batun kwaso yan Najeriya dake China ba

Majalisar wakilan Najeriya ta yi watsi da kiran da wasu suke yi na kwashe yan kasar  Najeriya da ke  kasar ta China, yayin da coronavirus ke bazuwa daga kasar ta China zuwa wasu kasashen  daban na duniya.

Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai Mr Benjamin Kalu, ne ya gabatar da kudirin inda ya nemi a kwaso ‘yan Najeriya da ke China sakamakon annobar ta coronavirus.

Sai dai   yan majalisar basu amince da kudirin ba, inda suka ce  gara a bar su a can kasar domin a cewar su, China ta fi Najeriya kayayyakin magance lamarin annobar coronavirus da ta bayyana.

 Kakakin majalisar  wakilai wato Femi Gbajabiamila, yayi kokarin wajen shawo kan yan majalisar da kuma bari Mista Okezie ya gabatar da kudirin nasa kan al’amarin, amma sam  yan majalisar basu yarda sun bada hadin kai da bashi damar yin hakan

 

 

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: