Coronavirus: CDC za ta baza ma’aikatan lafiya miliyan 1 a kasashen Afirka

Hukumar da ke dakile yaduwar cutuka a Afirka wato Africa CDC ta ce tana wani yunkuri na tura ma’aikatan lafiya miliyan 1 a kasashen nahiyar, nan da karshen shekarar 2020 domin yaki da cutar ta Covid19.

Hukumar ta Africa CDC, ta bayyana hakkan ne a shafin ta na tiwita.

A ranar Alhamis ne hukumar ta fara tura jami’ai 20 zuwa kasar Habasha wato Ethiopia domin taimaka wa kasar wajen yaƙar da cutar ta Coronavirus.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: