Coronavirus: Majalisa wakilai  ta bukaci tafiya hutun makonni 2

Yan majalisar tarayyar Najeriya sun bukaci tafiya hutun makonni biyu, bisa dalilin fargabar yiwuwar yaduwar cutar Coronavirus a majalisa, wacce ta bulla a Najeriya.

Majalisar tace zaka yi amfani da lokacin ne wajen yin duba game da irin shirin da gwamnatin tarayya ta yi a kasar.

Majalisar ta cimma matsayar dakatar da zaman ne bayan da Mista Josiah Idem ya gabatar da bukatar yin hakan a zauren majalisar a yau  Talata  2 ga watan Maris 2020,yayin da  sauran takwarorinsa suka amince da hakan.

Dan majalisar Kano, Ahmed Nasir ya bayyana damuwarsa a kan rashin isasun wuraren gwaje-gwajen cutar a Najeriya, idan barakar cutar ta kunnu kai, yayin da dan majalisar Kebbi Sununu Yusuf  ya yabawa wa NCDC kan irin shirin da datayi na hanzari wajen gwajin cutar ta coronavirus tare da kebe mai dauke da cutar.

 

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: