Coronavirus: NCDC bata bukatar yi mana gwaji – Ali Nuhu

Tauraron fina-finan Kannywood, Ali Nuhu, ya ce hukumomin lafiyar Najeriya sun shaida musu cewa shi da abokan aikinsa ba sa cikin hatsarin kamuwa da coronavirus.

Ali Nuhu ya shaida wa BBC cewa hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce ba a bukatar yi musu gwajin cutar.

Batun yi musu gwajin ya taso ne bayan kiran da gwamnatin jahar Lagos ta yi cewa duk wanda ya halarci bikin karrama jarumai da aka gudanar a birnin na Lagos ya je a yi masa gwajin coronavirus saboda ta gano cewa wani mai dauke da cutar ya halarci bikin.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: