Da Dimi-Dimi: Duk wanda ya fadi takara a mayar masa da kudin sa – Gwamnan Niger

Gwamnan Jahar Niger Abubakar Sani Bello yace duk wanda ya fadi takarar zaben fidda gwani, koh yake da matsala a jam’iyyar ta APC yana ganin  a mayar musu da kudaden su.
 
Gwamna Abubakar Bello ya baiyana hakan ne a gurin taron kwamiti da aka gudanar  na kara wa juna sa ni, wanda  yan takarkarun gwamnan, shuwagabanin  jam’iyya, sakatarorin jam’iyya tare da masu ruwa da tsaki a na jam’iyyar ta APC  na jahohi 36 a fadin  kasar ta Najeriya suka hallata, wanda shugaban jami’iyyar ta kasa, Adams Oshiomhole ya shugabanci taron a babban ofishin jam’iyyar APC dake babban birnin tarayya Abuja a ranar Al’hamis 6 ga watan Disamba 2018.

You might also like More from author

Comments are closed.