DA DUMI-DUMI: An rantsar da sabon mataimakin gwamna a jahar Kogi

An rantsar da Mista Edward Onoja a matsayin sabon mataimakin gwamnan jahar Kogi a yau Litinin, 21 ga Oktoba 2019  a gidan gwamnatin Lugard House dake Lokoja dake babbar birnin jahar.

An rantsar da Onoja ne bayan ya bayyana a gaban majalisar dokokin jahar, dan tantanceshi kafin a tabbatar da shi.

 Alkalin alkalai na  jahar Nasir Ajana, ne ya rantsar da shi.

Yayin da  gwamna Yahaya Bello, mambobin majalisar da manyan jami’an gwamnati suka hallarci wajen rantsuwar.

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: