DA DUMI- DUMI: DSS ta damke  shugaban EFCC Magu

Tun 2015 Zuwa yanzu ba’a tabbatar da nadin Magu ba, sakamakon rahotun da DSS ta saki wanda ke nuna rashin cancantar sa.

Rahotunni na nuna cewa, hukumar tsoro ta farin kaya a Najeriya  wato DSS  ta damke  shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu  a shedikwatar EFCC dake birnin Abuja a yau 6 ga watan Yuli 2020

Zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani kan dalilin yasa aka damke shi.

A kwanakin baya da suka wuce dai, ministan shari’a , kuma babban antoni janar na kasar Najeriya,  Abubakar Mallami ya tura da takardar  zuwa ga shugaban, kasa Muhammadu Buhari, wanda ke kalubalantar Magu bisa almundahana.

Mallami ya bukaci shugaba Buhari da ya
kori Magu daga aiki, bisa zargin siyar da wasu kadarori da aka dawo dasu, ba tare da sannin wani ba, musamman ma ma’aikatar sa da take da hakkin kula da ma’aikatar ta EFCC.

TheCable ta rawaito cewa, shugaban EFCC ya yi tafiya zuwa birnin Dubai  ba tare da  sanin shugaba Muhammadu Buhari ba, kuma a yayin  ake cikin dokar ta hana fita a  kasar.

Bayan an  tuhumeshi, ya ce ya je gudanar da  wani bincike ne.

 Ana zargin Magu wajen yin rayuwar da ta fi abinda yake samu daga aikinsa.

Sai dai mai magana da yawun Magu, Tony Amokeodo ya bayyana wa gidan talabijin na Channel cewa, ba kama shi DSS tayi ba,an gayyaci mista Magu zuwa gaban wani kwamiti da shugaban kasa ya kafa don duba, da kuma amsa tamboyoyi kan zarge-zargen da ake yi masa na almundahana.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: