DA DUMI DUMI – Ize-iyamu ne zabbaben dan takarar gwamna jahar Edo

Fasto Osagie Ize-Iyamu  ya samu nasarar zama zababben dan takarar kujerar gwamnan jahar Edo karkashin jam’iyyar APC, inda gwamna Obaseki yasha kaye.  Ize-iyamu, wanda tsohon sakataren gwamnatin jahar ne, kuma ya zama dan takarar ne bayan  da jigogin jam’iyyar suka yinke hukuncin hakkan  ranar Talata a  birnin Abuja.

Shugaban kwamitin tantance yan takarar, sanata Francis Alimikhena, ya gabatar da Faston a matsayin wanda ya wakilci jamiyyar a zaben.

Sauran mambobin kwamitin tantancewar sun hada da tsohon mataimakin gwamnan jahar, Lucky Imaseun, Janar Ceci Esekhaobe, Thomas Okosun, Samson Osagie, Patrick Obahiagbon da kuma Peter Akpatason.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: