DA DUMI-DUMI: Kotu ta yanke wa Olisa Metuh hukuncin zaman gidan yari na shekaru 7

Wata babbar kotu Najeriya da ke babban birnin tarayyar Abuja, ta yanke  wa tsohon kakakin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Olisa Metuh,hukuncin zaman gidan yari na shekaru Bakwai  kan  laifin almundahanar kudi naira miliyan 400.

Alkain kotun mai shari’a Okon Abang, a wajen yanke hukuncin a yau Talata 25 ga watan Fabrairu 2020 ya bayyana cewa ya kama tsohon jami’in na jam’iyyar PDP da dukkanin laifukan  guda 7 da ake tuhumar sa dashi na halatta kudaden haramun.

 Hukumar  yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya wato EFCC  ta shigar da shi kara, inda take zarge shi da karbar kudin daga hannun tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha’anin tsaro, wato Kanar Sambo Dasuki.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: