DA DUMI-DUMI: Najeriya na cikin manyen kasashen 10 dake da saukin kasuwanci

Najeriya ta shiga sahu na 131 a duniya cikin kididdigan bankin duniya na jerin kasashen da keda saukin kasuwanci, wanda hakan ke nufin tayi tsalle 15 daga sahun da take a 2019.

Cibiyar Bretton Wood ce ta bayyana hakan a cikin rahotonta da ta saki a safiyar ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoba.

 An samu wannan kididdiga ne bayan an harhada tare da kwatanta kamanceceniyar tsarin kasuwanci a kasashe 190 a fadin duniya.

 A baya babban bankin duniya ta ambaci sunan Najeriya a matsayin daya daga cikin manyan kasashe 20 da ke da saukin yin kasuwanci a fadin duniya,rahoton yace Najeriya na daga cikin manyan kasashe 10 a duniya,sannan kuma an ambaci sunayen kasashe irin su: Saudi Arabia, Jordan, Togo, Bahrain, Tajikistan, Pakistan, Kuwait, China da India duk a cikin manyan kasashe 10 dake da dadin kasuwanci a Duniya.

 

 

 

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: