DA DUMI-DUMI:Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar  APC  Abdulkadir  ya rasu

 Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar  APC na arewa maso yamma, Alhaji Inuwa Abdulkadir  ya rasuwa.

Marigayi Abdulkadir  ya kasance daya daga cikin mambobin  kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da aka rushe a yan kwanakin baya da suka wuce.

Jami’in hulda da jama’a na jami’ar
jahar Sokoto,Zayyanu Shehu, ya tabbatar da rasuwar, inda ya bayyana cewa za’a gudanar da jana’izar  marigayi  Abdulkadir a  gidansa dake Unguwar  Gawon Nama da misalin karfe 2 rana, a yau Litinin 5 ga watan Yuli 2020.

Marigayi Inuwa Abdulkadir ya rasu yana da shekaru 54, bayan ya sha fama da rashin lafiya, sai dai babu wata majiya akan wace irin cuta ce ta kashe shi.
 Inda ya bar mata 2 da kuma yara 9.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: