Dalilin da yasa Buhari ya hana rance ga masu shigo da shinkafa.

A cikin hirarshi da Sashen Hausa, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dake neman wa’adin mulki na biyu karkashin tutar Jam’iya mai mulki APC ya bayyana cewa, akwai banbancin tsakanin yadda ake samun wutar lantarki yanzu da yadda take shekaru hudu da suka wuce. Yace masu yin sana’oi suna shaida ci gaban da aka samu a wannan fannin wadanda a da suke amfani da janareta domin gudanar da sana’oinsu.

Shugaba Muhammadu Buhari yace kokarin gwamnatin yanzu shine maida hankali wajen neman hanyar samar da wuta dake amfani da rana domin magance matsalar fasa bututu da wadanda suke zaune a inda ake samar da iskar gas suke yi, da kuma gudun fuskantar karancinshi.

Dangane kuma da inganta harkokin noma, shugaba Buhari yace a shekarar dubu biyu da goma sha shida ya gayyaci ministan harkokin noma da kuma shugaban babban bankin duniya yace su nemi hanyar da zasu bi ta bada bashi ga manoma cikin sauki domin tallafawa masu karamin karfi ba tare da bin hanyoyin da aka saba bi ba, dake da tsawo kuma da wahalarwa ga kananan manoma. Banda haka kuma yace an samar da takin zamani isasshe wanda ya taimaka wa manoman wajen bunkasa harkokin noman nasu.

Shugaba Buhari ya kuma ce rufe kan iyakoki da gwamnati tayi da hana shigo da shinkafa ya taimaka wajen samar da shinkafa ta cikin gida, duk da cewa  har yanzu ana fuskantar tsadar kayan masarufi.

Shugaba Buhari yace tilas ne a yi maganin ‘yan sumogal idan ana son amfanin gona na cikin gida ya wadata, kuma a sayi abinda ake nomawa a cikin gida.

Dalili ke nan da ya sa ya umarci hukumomi kada su bada rance ga wanda yake neman shigo da shinkafa.

You might also like More from author

Comments are closed.