Dalilin da yasa gwamnatin  Neja ta amince a kashe wa   Almajirai  miliyan 86

Gwamnatin jahar Neja ta amince da kashe  naira  miliyan 86 domin killace Almajirai, ciyar da su da kuma mayar dasu jahohinsu asali.

Kwamishinar  Ilimin  ta jahar Neja, Hannatu Salihu, bayyana hakan ne a lokacin da take  hira da manema labarai a Minna, babbar birnin jahar, a ranar Laraba.

Inda tace  an yi hakan ne bisa shawarar da kungiyar gwamnonin Arewa ta yanke na mayar da Almajirai jahohin nasu na asali  a yukurin ta na guje wa yaduwar  annobar  cutar ta  Coronavirus.

A karon farko dai an mayar da Almajirai guda  86 jahohinsu kuma an hadasu da iyayensu,  inda a karo na biyu kuma, aka mayar da Almajirai 557 cikin 708 garuruwansu na asali.

Sannan kuma akwai yan kasashen ketare guda 12, sai kuma guda biyu da ba’a gano  ainihin jaharsu ba zuwa lokacin.Inji Kwamishinar lafiya ta Neja.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: