Dalilin da yasa na janye takarar shugaban majalisar wakilia – Gudaji

Dan majalisar wakilai mai wakiltar jahar Jigawa, Muhammad Gudaji kazaure ya bayyana a shifinsa na Instagram cewa, na janye bayyana takarar ta shugaban majalisar wakilai, wanda nake shirin gudanar wa a ranar Talata.

Gudaji yace, ya janye ne saboda umarnin da gwamnan jaha ta, Mohammed Badaru Abubakar tare da shugaban kasar Najeriya Muhamadu Buhari suka yi mini, na cewa mu girmama jam’aiyyar APC tare da abun da ta tsayar wa yan jam’iyyar.

Hakan ya sa nake kira ga magoya bayana da su yi hakuri inji shi.

You might also like More from author

Comments are closed.