Dalilin da yasa na sauya sheka zuwa PRP – Sagir Takai

Dan takarar gwamna a jahar Kano Salihu Sagir Takai ya ce ya sauya sheka daga PDP zuwa PRP ne sakamakon rashin adalci da ke gudana a jam’iyyar ta PDP.

Dan siyasar wanda a baya aka bayyana shi  a matsayin dan takarar gwamnan jahar Kano a karkashin  inuwar jam’iyyar  PDP, sai dai a yanzu  ya sanar sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa  PRP.

A makon da ya gabata ne dai ta bayyana cewa Abba Kabir Yusuf wanda bangaren Kwankwasiya ke ra’ayi aka tsayar a matsayin dan takarar jam’iyyar ta PDP a Kano, ba Malam Salihu Sagir Takai ba.

Hakan yasa Takai ya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar PRP, inda yake cewa  son kai  rashin adalci da suke  nunawa ba  dadai bane “Mun wayi gari a PDP ana yin abin da aka ga dama ba tare da an tafi da ‘yan jam’iyya ba,” in ji shi.

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: