Dalilin dayasa Rarara yaifada da Baban Chinedu

Tabbas har yanzu jam’ar Najeriya musamman ma na arewacin ta na ci gaba da mamakin yadda kwatsam aka dena jin shahararren mawakin nan na jam’iyyar APC da Buhari watau Dauda Kahutu Rarara tare kuma da abokin wakar sa Baban Chinedu a waka tare To sai dai binciken mu ya gano mana cewa duk da yake cewa shahararrun mawakan kuma masu nishadantarwa sun fito ne daga jiha daya watau Katsina

Kuma abotar su ta dade, dukkan kokarin da na kusa da su sukayi domin ganin an sasanta su abin ya citura. 

Musabbabin abun da ya hada su dai kamar yadda ake ta rade-rade ba zai wuce harka ta kudi ba da aka ruwaito cewa wai sun samo a wajen wani wasan da suka yi a kasar jamhuriyar Nijer. Mun dai samu labarin cewa a wajen wasan, wasu manyan yan siyasar kasar suka ba su kudin amma a wajen rabon sai shi Rarara ya bukaci na shi kason ya fi yawa don kuwa shine yafi shahara kuma aka fi sani,

zance da shi kuma Baban Chinedu aka ce bai lamunta ba. Daga karshe ne kuma dai sai Baban Chinedu din ma aka ce ya bar ma Rarara dukkan kudin.

You might also like More from author

Comments are closed.