Dan majalisar wakilai na Jamiyar PDP daga jihar Adamawa ya canza sheka zuwa APC

Mamba Mai wakiltar mazabar Madagali/Michika a majalisar wakikai ta tarayya Adamu Kamale na Jamiyar PDP ya canza sheka zuwa jamiyar APC, ya bayyana komawar tasa a wata wasika da kakakin majalisar Yakubu Dogara ya karanta a zauren majalisar. Mr Kamale yace rikicin daya dabaibaye jamiyar PDP shine yasa shi ya koma APC. Shine Dan majalisa daya tilo daga jamiyar PDP a jihar ta Adamawa.

You might also like More from author

Comments are closed.