Dokar hana fita ta kare a jahar Kano

Gwamnan jahar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya janye dokar hana fita a jahar.

Ma’aikatar lafiya ta jahar ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter ranar Alhamis 2 ga watan Yuli 2020.

Gwamnatin ta ce ma’aikata daga mataki na 12 zuwa sama za su koma aiki daga ranar Litinin 6 ga watan Yuli.

Sannan ana ci gaba da tattaunawa kan ranar da za a bude makarantu ga dalibai da ke shekarar karshe da masu rubuta jarrabawar kammala aji uku da ‘yan firamare masu rubuta jarabawar shiga sakandare.

Haka zalika cire wannan doka na nuni da cewar an bude dukkan guraren da aka kulle a baya amma dole su tabbatar da matakan kariya a guraren harkokinsu kamar yadda hukumomin lafiya suka umarta, a cewar kwamishinan yada labarai na Kano wato Malam Muhammad Garba

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: