Dokar hana zirga-zirga a Jahar Kaduna ta dawo Sabuwa

Gwamnatin jahar Kaduna ta sabonta dokar hana zirga-zirga a cikin garin Kaduna a safiyar yau Juma’a da misalin karfe 11:00,  dokar ta tsawon awanni 24 za ta fara aiki da karfe 11 daidai ne zuwa gobe Asabar.

An sanya dokar ne bayan da aka samu rahoton mutuwar basaraken da masu garkuwa suka kama a makon da ya wuce, an samu rahoton mutuwar Mista Maiwada Galadima ne da safiyar yau Juma’a,

labarin mutuwar basaraken ta tada hankulan al’umma da dama, hakan yasa rikicin ke neman barkewa yazama sabo ke neman haifar da wani sabon rikici a garin na Kaduna.

A bukaci al’umma su rungumi zaman lafiya, saboda wannan abu ne da wasu daga cikin  bata gari ne  suke  ai’katan hakan , kuma suna iya aikata hakan akan kowa, duba da ba kisa bane na bangarenci.

You might also like More from author

Comments are closed.