Dole Ne A Shawo Kan Yadukar Makaman – Saraki

Biyo bayan yawaitar makamai a hannun jama’a ba bisa ka’ida ba, Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci shugabannin rundunonin tsaron kasar su bayyana gabanta.

A kokarin Majalisar Dattawa na samar da hanyar da za a bi wajen gano tare da daukar matakin hana yaduwar makamai a fadin kasar, shugaban Majalisar Abubakar Bukola Saraki, ya ce dole ne a shawo kan yadukar makaman a akasar.

Sai dai kuma kakakin rundunar sojojin Najeriya, Janar John Agim, na ganin wannan bincike ne da yakamata ‘yan sandan kasar su gudanar, don gano ta wacce hanya makaman ke shiga Najeriya.

Tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kano, Kanar Aminu Isah Kwantagora, ya ce tun lokaci da rundunar hadakar ta soviet union ta rushe, kowanne soja ya koma kasarsa suka bar makamansu, hakan yasa masu fataucin makamai suka bazu suna cin karensu babu babbaka.

Haka kuma lokacin da aka kashe shugaban kasar Libiya Mohammad Gaddafi, makamai sun kwarara kasashen yammacin Afirka.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: