DSS ta damke matar da take damfara da sunan Aisha Buhari

Hukumar tsaro farin kaya ta DSS ta kasar Najeriya ta damke mai damfarar mutane da sunan Aisha Buhari.
A cewar hukumar, Amina Mohammmed itace matar ta rika yi wa wasu manyan jami’an gwamnati sojan-gona — ciki har da matar gwamnan jahar Kogi.

Kakakin hukumar tsaro ta farin kaya, Peter Afunaya, ya ce matar tana amfani da sunaye daban-daban domin shiga cikin fadar shugaban kasar,kuma tana shiga ne ba tare da izini ba.

Sai dai kakakin DSS ya ce ana zargin matar da damfarar wani dan kasuwa naira miliyan 150 a shekarar 2017.
Ya ce ta rika amfani da sunan Aisha Buhari wajen damfarar mutane masu neman kwangila a fadar shugaban kasa.

You might also like More from author

Comments are closed.

Subscribe to our mailing list and get interesting stuff and updates to your email inbox.