EFCC Na Dab Da Gurfanar Da Diezani Alison A Gaban Kotu

 

Hukumar EFCC za ta gurfanar da tsohuwar ministar man fetur ta kasar, Mrs Diezani Alison-Madueke a gaban kotu kan zargin cin hanci da rashawa.

Mai magana da yawun hukumar Mr Tony Orilade ya fitar da sanarwa na cewa a watan Fabrairun 2019 ne za a gurfanar da Mrs Alison-Madueke da kuma tsohon shugaban kamfanin tatar mai na Atlantic Energy Drilling Company, Jide Omokore kan zargin aikata laifuka biyar.

A cewar EFCC, ana zargin mutanen biyu da karbar hanci da kyautuka a wurare biyu, dukka a birnin Lagos, hakan ya saba wa dokar hana karbar cin hanci da rashawa.


Inda EFCC ta kara da cewa ta samu izinin gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu daga mai sharia Valentine Ashi ta babbar kotun birnin tarayyar Abuja a ranar 3 ga watan Disamba.
Hukumar ta nemi izini gurin kotun domin ta samu damar taso keyar Mrs Madueke daga Burtaiya inda take zaune tun shekarar 2015.


Yayin da EFCC ta shaida wa kotun cewa dama ta dade da aike wa tsohuwar ministar takardar gayyata zuwa Najeriya domin ta kare kanta daga zarge-zargen cin hancin da ake yi mata saidai ta ki amsa gayyatar.

You might also like More from author

Comments are closed.