Yaki Da Rashawa: EFCC Ta Kwato Naira Biliyan 473 A 2017

Magu ya ce, tsakanin watan Janairu zuwa Disamban bara, EFCC ta gano sama da Naira biliyan 473 da Dala miliyan 98 da Euro miliyan 7 da kuma Pam miliyan dubu 294.

Mukaddashin shugaban ya bayyana wadannan alkaluman ne a yayin wani zaman jin bahasi kan kasafin kudin hukumar da kwamitin yaki da almundahnaa na Majalisar Wakilan Najeriya ya shirya.

Magu ya shaida wa mambobin kwamitin cewa, daga cikin kudaden da suka gano sun hada da Naira biliyan 32 da Dala miliyan 5 da aka kwace daga hannun tsohuwar ministar man fetir, Diezani Alison Madueke.

Ibrahim Magu ya shaida wa ‘yan Majalisar cewa, EFFC ta sanya dukkanin kudaden da ta kwato a cikin asusun gwamnatin tarayyar Najeriya.

Magu ya nuna takaicin a kan yadda ba a sake wa hukumar kudaden da ta kasafta domin yin aiyukanta, ‘Wannan yana matukar kawo mana cikas wajen gudanar da aiyyukanmu yadda ya kamata mussamma na zuwa sassan kasan nan domin gudanar da bincike.

A shekara 2018 fta mun kashe Naira Biliyan 45 amma an rage zuwa Naira Biliyan 21 wannan tabbas zai yi matuka takura wa aiyukanmu.

You might also like More from author

Comments are closed.