Firai Ministar Birtaniya Theresa May za ta yi murabus 7 ga watan Yuni

Firai Ministar Birtaniya, Theresa May ta bayyana cewa za ta ajiye mukaminta a ranar 7 ga watan Yuni domin ta bayar da damar a zabi sabon Firai Minista.

A cikin wani jawabi mai sosa rai da ta yi a titin Downing, Misis May ta bayyana cewa ta yi iya kokarinta domin ta karrama sakamakon zaben raba gardama na Tarayyar EU da aka yi a shekarar 2016.

Ta kara da cewa ba ta ji dadin rashin ganin ficewar Birtaniya daga tarayyar Turai ba.

Amma zaben sabon Firai Minista shi ne abin da ya kamata a yi a kasar nan yanzu.

Misis May ta ce z ata ci gaba da zama Firai Minista a yayin da jam’iyyarta ta Conservative take gudanar da zaben sabon Firai Minista.

Za ta sauka  a ranar 7 ga watan Yuni kuma za a fara wata fafatawar neman maye gurbinta, bayan ta sauka da sati daya

Muryar Mrs May ta yi rawa lokacin da take kammala jawabinta a inda ta ce: ”Zan ajiye mukamin da na yi farin ciki da rikewa.

”Firai Minista mace ta biyu, amma tabbas ba ta karshe ba,” in ji ta.

You might also like More from author

Comments are closed.