FRSC ta shawarci matafiya bikin Easter

Sashen Itori na hukumar kare hadurra ta kasa wato FRSC dake jahar Ogun sun shawarci mafiya a motoci da su yi tuki cikin hankali da bin dokokin tuki domin kaucewa fadawa hatsura akan hanya musamman a irin wannan lokacin da wadansu ke tafiya tafiyan bukukuwan Easter.

Kwamandan sashen, Sunday Oko, shi ne ya ba da wannan shawarar a yayin zantawarsa da manema labarai a garin Ota dake Ogun a yau Litinin 15 ga watan Afrilu.

Rahotanni sun nuna cewa; mabiya addinin Kirista a duk duniya, za su yi bikin Easter a ranar 19 zuwa 22 ga watan Afrilun shekararnan.

Wanda wannan bikin suna yinsa domin tunawa da Yesu Almasihu da kuma fatan tashinsa da za a sake yi.

Oko ya nemi  direbobi su  daure wajen ganin sun bi dukkanin ka’idojin tuki musamman dokar tuki ta kasa na shekarar 2012, inda ya yi gargadi da cewa; duk wanda aka kama ya karya dokar tukin, to doka za ta yi aiki a kansa.

A karshe ya shawarci direbobi ‘yan kasuwa da su tabbata da lafiyar motocinsu kafin su dauki mutane zuwa inda za su je domin bikin Easter.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: