Ghali Na’abba ya fita daga jam’iyyar APC

Tsohon kakakin majalisar wakilai Ghali Na’abba  ya baiyana sanarwar fice wa daga  jam’iyyar APC.

Ghali ya bayyana cewa chakwakiyar  dake cikin jam’iyyar APC yasa ya fice daga  jam’iyyar a doguwar wasika da ya rubuta.

Rashin iya  tafiyar da ‘yan jam’iyya a matsayin tsintsiya madauri daya ya haddasa abubuwan da suka faru a majalisar kasar ta Najeriya, har ya janyu jam’iyyar ta rasa shugaban majalisar dattawai wato Bukola Saraki, inda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar ta PDP.

Ghali yace yayi kokarin ganin an samu gyara  a duk wata baraka dake tattare da jam’iyyar amma abun yaci tara.

Sai dai Ghali bai baiyana jam’iyyar ta zai koma ba.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: