Gwamna jahar Bauchi ya killace kansa sakamokon hada jirgi da dan Atiku

Gwamnan jahar Bauchi Bala Muhammad ya killace kansa tun bayan hada jirgi da ya yi da dan gidan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar wanda ya kamu da cutar Coronavirus.

Mai magana da yawunsa, Ladan Salihu ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ladan ya ce “mun hau jirgi daya da dan gidan na Atiku daga Lagos zuwa Abuja, inda suka yi musabiha hannu da hannu. .

Tuni aka yi wa gwamna da mu ‘yan tawagarsa gwaji. Muna fatan sakamakon gwajin zai yi kyau.”

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: