Gwamnan jahar Nasarawa ya rattaba hannu a dokar kisa ga masu garkuwa da mutane kuma ya haramta bara a jahar

Gwamnan jahar Nasarawa, Abdullahi Sule ya haramta bara a titunan jahar, yayin da kuma ya rattaba hannu a dokar kisa ga masu garkuwa da mutane

Batun hana bara a  jahar Nasarawa:

Gwamna Abdullahi ya bayyana hakan ne yayin rantsar da hukumar kare hakkin wanda aka gudanar  birnin Lafia.

Idan yace, ba tare da nuna gadara ba dokar ta hana bara a tituna ta tanadi hukunci ga iyayen da suka watsar da nauyin da ke kansu, hakan yasa gwamnatin ta dauki matakin saka yaran da ke karatu a Tsangaya cikin karatun boko don magance matsalar.

Sannan ya kuma tabbatar da dokar bada kariya ga yaran da kuma tabbatar da tsaro, kiwon lafiyarsu, iliminsu tare da yin  kira ga shugabannin gargajiya, addinai kuma da jama’a da su goyi bayan lamarin wajen ganin jahar a zamu cigaba.

Batun rattaba hannu a dokar kisa ga masu garkuwa da mutane:

Gwamna Abdullahi Sule, ya rattaba hannu a kan dokar zartar da hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a jahar ta Nasarawa.

Majalisar dokokin ta jahar ta gudanar da mahawara tare da yin kwakkarar duba a kan lamarin kafin amincewa da dokar.

Dokar ta ayyana laifuka masu nasaba da garkuwa da mutane da hukunce-hukuncen da ya kunsa. Daga cikin hukuncin akwai dauri a gidan yari da hukuncin kisa, sannan kuma gwamnatin jahar  za ta mallake duk wata kaddara ta wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane, haka kuma  duk masu bayar da hayar wuraren zama ga masu garkuwa da mutanen, suna iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari cewar gwamna Abdullahi Sule.

 

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: