Gwamnatin jihar Oyo ta fara lika hatimin gargadi dan mallakar kwadon shara

Gwamnatin ta ce za a rufe gidan da ya ki bin wannan umarni tare da kama mai gidan da za a yanke masa hukumcin daurin wata 6 ko tarar Naira dubu 50.

Kwamishinan ma’aikatar muhalli da samar da ruwan sha na Jihar Oyo, Mista Isaac Ishola ne ya fadi haka a ganawarsa da ’yan jarida a Ibadan. Ya ce, yawaitar bola a kan hanyoyi da zubar da shara barkatai su ne suka sa gwamnati ta dauki wannan mataki na yin gargadin na kwana uku ga dukkan gidaje da wuraren kasuwanci domin wayar da kan jama’a a game da wannan doka.

Kwamishinan ya ce yanzu haka jami’an duba-gari sun fara shiga cikin gidajen mutane da wuraren kasuwanci da za su sanya idanu wajen lura da gidajen da suka kasa tanadar kwandon shara domin tsaftace muhallansu. Ya ce za a kama dukkan mutumin da ya ki samar da kwandon zubar da shara a gidansa tare da cin tarar kudi Naira dubu 200 ga dukkan masu kunnen kashi da suka bijire wa dokar.

Da yake karin haske, cewa ya yi yin haka ya zama wajibi saboda irin yadda mutane da ke zaune a manyan garuruwa a jihar suka mayar da matsugunansu da wuraren kasuwancinsu a kazance da zubar da shara a kan hanyoyi barkatai ba tare da tunanin irin illar da hakan ke haifarwa ga lafiyarsu ba.

Ya lissafo sunayen wasu unguwanni a cikin birnin Ibadan da suka hada da Oje da Ojoo da Sango da Moniya da Akingbile da Olode, wadanda ya ce su ne a kan gaba wajen zubar da shara barkatai. Ya ce daga yanzu sabuwar dokar za ta yi aikin ba-sani-ba-sabo ga dukkan wanda aka kama da laifin kasa tsaftace muhalli. Ya nemi jama’a su bayar da hadin kai ga wannan tsari domin amfanin kansu.

You might also like More from author

Comments are closed.