Gwamnatin tarayya ta amince da nadin Kaftin Rabiu Hamisu Yadudu

Shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari ya amince da nada Kyaftin Rabiu Hamisu Yadudu  a matsayin sabon Manajan Daraktan hukumar kula da tashoshin jiragen saman kasar ta  Najeriya wato FAAN.

Kyaftin Yadudu zai maye gurbin Injiniya Saleh Dunoma wanda aka dakatar, kamar yadda mataimakin Daraktan hulda jama’a da sadarwa na ma’aikatar sufuri (Sashen jiragen sama) James Odaudu, ya sanar a ranar litinin 20 ga watan Mayu 2019

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: