Gwamnatin tarayya ta baiwa kungiyar ASUU naira biliyan 15.4

Gwamnatin tarayyar Najeriya da Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU sun yi tattaunawar  kulla yarjejeniya ranar Litinin akan yajin aikin gama  gari da kungiyar take yi.

Ministan qwadago na Najeriya Sanata Chris Ngige ne ya jagoranci tattaunawar da aka yi a  babban birnin tarayyar ta Abuja.

Yayin  da sanata Ngigie ya ce, sun kai karshen yarjejeniyarsu tsakaninsu da kungiyar ASUU, Gwamnatin tarayya  at ba wa kungiyar ASUU Naira biliyan 15.4 don kungiyar ta samu damar biyan albashi ma’aikata, wanda  hakan ya na daya daga cikin bukatun kungiyar.

 

You might also like More from author

Comments are closed.