Hakkoki 21 Na Mace A Kan Mijinta

Akwai hakkokin da Musulunci ya dora wa miji daga lokacin da aka daura ma sa aure da matarsa.

1. Ya biya ta Sadakinta na Aure.

2. Ya kula da Addininta.

3. Ya daukin nauyin cinta, shanta, suturarta, har da kayan kwalliya nata. 4. Ya ba ta hakkinta na aure.

5. Ya dauki nauyin kulawa da lafiyarta.

6. Ya daukin nauyin karatunta musamman ma na Addini.

7. Ya nuna mata soyayya a fili.

8. Ya rika mu’amala da ita a cikin sauki kamar karamar yarinya.

9. Idan ya shigo gida ya rika sakar mata fuska da fara’a.

10. Ya rika yaba mata idan ta yi abin kirki tare da yi mata Addu’a ta fatan Alkhairi.

11. Ya rika sauraron korafe-korafenta da shawarawarinta.

12. Ya rika yafe mata idan ta yi masa ba dai-dai ba, kuma yana gyara mata cikin hikima.

13. Ya rika yin kwalliya da ado domin ta gani ta ji dadi.

14. Ya ba ta lokaci na musamman a lokutansa domin yin hira da ita kawai. 15. Ya rika cin abinci tare da ita.

16. Ya ringa taimaka mata wajen aiyukan gida musamman idan ta samu rauni na laulayin ciki ko na rashin lafiya tare da tausaya mata.

17. Ya rika nuna damuwa cikin abin da ta damu da shi, da farin a cikin abin da take farin ciki da shi matukar bai saka wa Allah ba.

18. Ya girmama iyayenta da ‘yan uwanta.

19. Ya ringa yi mata kyuata ta musamman domin faranta mata rai. 20. Ya rika fita da ita wurare na musamman kamar ziyara ko wurin karatu ko wurin shakatawa.

21. Ya rika boye aibinta. Allah Ya ba su ikon sauke wannan hakki da aka dora masu Wani Bawan Allah ya yi wa dansa nasiha da Da ya je wajen wasu Dabbobi guda hudu, Amma kar ya je sai bayan ya mutu.

Dabbobin da ya umarce shi ya je wajen su su ne:-

1- Doki.

2- kiyashi.

3-Maciji.

4-Kare.

Bayan mahaifinsa ya Rasu sai ya fara zuwa wurin Doki ya ce, Baba ya ce in ya mutu in zo Wajen ka. Doki ya ce Babanka yana da hikima, ka san abin da ya sa ya ce ka zo Waje na?

Yaro ya ce a’a, Sai Doki ya ce kalli inda nake zaune ya Duba ya ga wajen duk ya b aci da kashinsa, ga jikinsa duk datti, sai ya ce kalli wancan Matashin dokin Sai ya ga wajensa a share an yi masa wanka ga ciyawa mai kyau da ruwa a gabansa.

Sai Doki ya ce kaga yanzu ni na tsufa bani da wani amfani shi ya sa aka kyale ni a wulakance, shi kuma Matashin doki yana da karfin jiki, ana da bukatarsa shi ya sa ake kula da shi don haka babanka yana yi maka nasiha da ka mori kuruciyarka wajen abin da zai amfane ka.

Domin lafiyarka da kuruciyarka mutane suke bukata in ka tsufa ba ruwan kowa da kai. Daga nan sai yaje wajen kiyashi ya yi Masa bayani kamar yadda ya yi wa doki. Kiyashi ya ce, zo mu je suka je wajen mushan kyankyaso, yayi kokarin ya jawo shi shi kadai ya kasa, sai ya je ya kirawo yan’uwansa, suna zuwa suka janye Shi. ya ce babanka yana nufin komai zaka yi ka hada kai da ‘yan uwan ka kar ka yi kai kadai.

Daga nan sai ya je wajen Maciji Ya tarad da shi a cikin kogo a lab e, nan ma ya yi masa bayani, maciji ya ce ce, ka ganni a b oye, yanzu ma yunwa nake ji, da zan fita a ganni kashe ni za’a yi, sai dare yayi, sahu ya dauke, nake fita, kuma ba wani abu ne ya jawo min wannan bakin jinin ba sai bakina da Harshena. Babanka yana nufin ka iya harshanka, ka kiyayi barin zance. Daga nan sai ya je wajen kare shi ma ya yi masa bayani, sai ya ce, zo mu je cikin gari, suna zuwa sai yara suka fara jifan kare, da kyar suka sha, sai kare ya ja shi wajen mafarauta suna Zuwa sai Suka fara Murna suna kiransa Da sunaye kala-kala, wannan ya jefa masa nama wannan yana shafa shi yana dariya. Sai kare ya ce baban ka yana nufin ka-kasance cikin wadanda suke sonka Kuma, ake ganin Mutuncinka,

Maganin Cutar Koda Cutar koda a wannan zamanin ta zama ruwan dare, saboda Allah kadai ya san yawan mutane da ta yi sanadiyyar ajalinsu, saboda haka yan’uwa kuzo mu taimaka muceci rayuka daga halaka asanadiyyar cutar koda.

A jaridar UKAZ dake garin Falasdinu an rawaito cewa, saurayi mai shekaru 35 ya warke daga cutan koda bayan an yi masa wankin koda (dialysis ) na tsawon shekara daya abin bai yi ba, sai sanadiyyar amfani da (Karo) likitan ya tabbatar masa da cewa yawarke har abada, kuma baya bukatar wankin koda nan gaba.

Sannan har yanzu an samu wata yarinya mai shekaru 21 wanda ta samu wannan matsalar kodar, aka je aka yi mata gwaji a asibiti, ‘Creatinine’ na ta ya hau zuwa 550, amma sai ya ragu ya koma 200 bayan ta yi amfani da Karo natsawon mako uku kacal. Misalai irin wannan suna da yawa, saboda haka ya zama dole yan’uwa su yada wannan bayani saboda kowa ya karu. To Yaya Za A Yi Amfani Da Shi?

Za’a nika karon ko a daka sosai har ya yi laushi, daga bisani sai adebi cikin babban cokali biyu da safe a zuba a ruwa kofi daya sai a barshi kamar awa biyu ko uku har ya narke sai a gauraya sosai asha da safe kafin Karin kumallo, sannan a maimaita haka da yamma sai asha kafin bacci. Kalar Karon Da Za Ku Yi Amfani Da Shi: Zaku samu asalin karo na itacen karo wato (Kolkol) da shi ake yin amfani. Haka za’aci gabada amfani da shi har a samu sauki, domin karo ba ta da cutarw

You might also like More from author

Comments are closed.