Hayar mutane PDP tayi zuwa jahar Sokoto – Gwamna El’Rufa’i

Gwamnan Jahar Kaduna Nasiru El-Rufai  ya ce yawancin mutane da suka taro a jahar Sokoto wurin taron kaddamar da kamfen din dan takarar shugaban kasar Najeriya karkashin inuwar jam’iyyar PDP hayo su akayi daga kasa  Nijar.

Gwamna El-Rufai yace jam’iyyar ta  PDP gani tayi  mutanen Sokoto ba za su halarci gurin taron nasu  hakan yasa suka hayo wasu mutane daga kasar Nijar dan ganin taron nasu yayi armashi.

Nasiru  El-Rufai ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da kwamitin Kamfen din jam’iyyar APC da akayi a garin Kaduna a ranar Talata 4 ga watan Disamba 2018.

 

Inda ya kara da cewa ranar da shugaba Buhari zai isa jahar ta Kaduna to ina tabbatar muku da cewa mutanen Kaduna ne zasu tare ba haya zamu yi ba, sannan kuma ” Za mu bi kuri’u dalla-dalla domin ganin APC ta lashe zabukan na 2019 mai gabatowa  a jihar Kaduna ba tare da wami tashin hankulam al’umma ba.

A karshe ya kara da cewa  yana so ya sanar wa da al’umma  cewa gwamnatin  shugaba Buhari ba gwamnatin barayi bace ,sannan kuma ba gwamnati da za ta rika yin wadaka  kudi ko almubazzaranci ba.

Gwamnati ce da take kashe kudaden ta wajen ganin ta inganta rayukan ‘yan Najeriya.

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: