Hukumar Alhazai ta shirya wa jami’anta taro dagane da aikin hajji

Hukumar lura da aikin hajji ta kasa, wato NAHCON ta shirya wa manyan jami’anta taron horaswa na kasa na kwana guda dangane aikin hajji a ranar 24 ga watan Afrilun 2019, a jahar Kano.

Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar, Fatima Usara ta bayyana hakan a birnin tarayya Abuja.

Inda taron na wannan lokacin aka yi masa take da, “Towards Achiebing Acceptable Hajj.’ Wato ma’ana hanyar cimma nasarar yin hajji karbabbe.

Ta bayyana cewa, manyan jami’anta masu ruwa da tsaki za su halarci taron.

Usara ta ce, taron zai yi duba ne ga muhimmancin da ke cikin Hajjin ta yadda zai taimakawa mahalarta fahimtar abubuwa da dama dangane da hajjin 2019.

Kuma zai horas da mahalartar dangane da ‘yancin da mahajjaci yake da shi tun kama daga filin jirgin sama har kan wadanda ya kamata su tsaya musu.

Sannan har wala yau za a horas da mahalarta taron dangane da dokokin kasar Saudiyyah.

Ta tabbatar da cewa ana fatan wadanda za su amfana da wannan horaswar za su isar da sakon taron zuwa ga mahajjatan yankinsu.

You might also like More from author

Comments are closed.