Hukuncin zaben Bayelsa: Oshiomhole, Diri Duoye, Degi sun hallara a kotun kolin Najeriya

A yau 26 ga watan Fabrairu ne Kotun kolin Najeriya take zaman sake duba a shari’ar zaben gwamnan jahar Bayelsa  wanda na jami’yyar All Progressive Party (APC) ta bukata.

Jam’iyyar APC ta bukaci kotun ta janye hukuncin  data zartar na kujerar daga hannun dan takarar gwamnan APC, David Lyon.

Shugaban jam’iyyar APC, Adam Oshiomole, gwamnan jahar Bayelsa, Duoye Diri, Sanata Degi, da sauran jiga-jigan yan siyasa sun hallara a kotun domin ganin yadda zata kaya.

Kwamitin Alkalan kotun koli bakwai karkashin jagorancin Alkali Sylvester Ngwuta zai saurari karar.

Lauyan David Lyon, Afe Babalola, ya yi kira ga kotun ta janye hukuncin da ta zartar na ranar Alhamis13 ga Febrairu 2020, domin kuwa  rufa-rufa a hukuncin.

 

 

You might also like More from author

Comments are closed.

%d bloggers like this: